Sakamakon zaben Mali | Labarai | DW | 18.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben Mali

Gungun jam'iyyun masu mulkin kasar Mali sun samu galaba a zaben majalisar dokokin da ya gudana ranar Lahadi da ta gabata.

Jam'iyya mai mulkin kasar Mali da wadanda suke kawance, sun lashe kujeru mafi yawa na majalisar dokokin kasar, a zaben da ya gudana ranar Lahadi, wanda ke zama matakin karshe na komawar kasar bisa tafarkin demokaradiyya.

Jam'iyyar RPM ta Shugaba Ibrahim Boubakar Keita take matsayi na farko bayan zaben zagaye na biyu, inda ta samu kujeru 61 daga cikin 147 da majalisar dokokin ta kunsa. jam'iyyar Adema mai alaka da mai mulki take matsayi na biyu da kujerun majalisa 20, kamar yadda wani babban jami'i ya tabbatar. Jam'iyyar URD ta Soumaila Cisse tsohon dan takarar shugaban kasa ta samu kejeru 18. A gaba jam'iyyu masu mulki sun samu kujeru 115 daga cikin 147.

Cika wannan sharadi na kammala zabukan zai bai wa kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka, damar samun kudade fiye da dala bilyan uku daga masu bayar da agaji.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu