Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Cyprus
February 17, 2013Sugaban jam'iyyar Disy, Nicos Anastasiades mai shekaru 66 da haihuwa, ya lashe kashi 45 cikin ɗari a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar yau a Cyprus, a yayin da abokin hammayarsa, Stavros Malas na jam'iyyar AKEL communist , ya samu kashi 27 cikin ɗari, sai kuma tsohon Ministan kula da harkokin ƙasashen wajen ƙasar, George Lillikas ya tashi da kashi 25 a cikin ƙuri'un da aka kaɗa.
Saɓanin yadda alƙalluman farko suka nunar , a yanzu cilas aje zagaye na biyu ranar Lahadi mai zuwa tsakaain 'yan takara biyu da ke kan gaba wato Nocos Anastasiades da Stavros Malas.
A tarihin ƙasar Cyprus zaɓen wannan shekara ,na da muhimmanci sossai, ta la'akari da matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta, da kuma matsalar tsuke bakin aljihun a ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai
Babban ƙalubalen da ke a gaban wanda zai lashe zaɓen , shi ne farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da ya shiga halin tsaka mai wuya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Saleh Umar Saleh