SADC Zimbabwe | Siyasa | DW | 25.06.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SADC Zimbabwe

Taron Ƙungiyar SADC a game da rikicin siyasa a Zimbabwe

default

Rikicin siyasa a Zimbawe


Yau ne Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin kudancin Afrika, wato SADC ta shirya zaman zato na mussamman, da zumar lalubo hanyoyin  warware rikicin siyasar ƙasar Zimbabwe.

Wakilin DW a yankin kudancin Afrika Stäcker Claus, ya rubuta rahoto a game da wannan ƙiƙi-ƙaƙa, wanda kuma Yahouza Sadissou Madobi ya fassara mana.


Ranar juma´a mai zuwa ce aka tsara shirya zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu  a Zimbabwe ,to saidai ta la´akari da matsaloli iri iri da kuma ƙuntatawar da adawa ke fuskanta, ɗan takara Morgan Tchangirai ya yanke shawa ƙauracewa, kuma ya zuwa yanzu ya na zaman gudun hijira a opishin jikadanci Holland dake birnin Harare.

A sakamakon  badaƙallar dake wakana, Majalisar Dinkin Duniya, Ƙungiyar Tarayya Turai, Amurika da Ƙungiyar SADC, suka yi kira ga shugaba Robert Mugabe ya ɗage wannan zaɓe har sai an samu  masalaha tsakanin ɓangarorin biyu.

To saidai Mugabe ,yayi kunnen uwar ya kuma cigaba da yaƙin neman zaɓe.

"Za mu shirya zaɓenmu, mutane su faɗi abunda suka ga dama, zaɓenmu namu ne, ba nasu ba, kuma ƙasar mu ƙasa ce mai cikkaken´yanci."

Ƙungiyar SADC ta wakilici shugaban ƙasar Afrika ta Kudu Tabon Mbeki ya shiga tsakanin wannan taƙƙadama, to saidai jama´ a da dama na zargin Mbeki da nuna fifiko ga shugaban Robert Mugabe.

A yanzu haka akwai minista ɗaya na gwamnatin Mbeki, dake birnin Harare, inda yake tattanawa da ɓangarorin biyu, a game da haka, ya zama wajibi a saurarai sakamakon tattanawar, inji jikadan Zimbabwe  a Afrika ta Kudu Khaya Moyo:

" Ƙungiyar SADC ta naɗa wakili, wato Tabon Mbeki, wanda ke aiki wurjenjen, domin  gano bakin zaren warware  rikicin, muna fata ya cimma nasara, ko da shike katsa ladan daga ƙetare na  maiyar da hannun agogo baya a yunƙurin cimma burin da  aka sa gaba."

A nata gefe, jam´iyar MDC mai adawa bayan ta yanke shawara ƙauracewa zaɓen, ta kuma ce ba zata taɓa hawan tebrin shawara ba, da Robert Mugabe, a daidai wannan lokaci da shugaba  Morgan Tchangirai ke cikin halin gudun hijira, sannan Tendai Beti, babban Sakatare Janar na Jam´iyar MDC ke tsare a kurkuku.

Roy Bennett, jigo  a jam´yar MDC ya bayyana ƙarin dalillan da suka sa su yanke wannan shawara.

"Kwata kwata babu batun tattanawa, mudun Tendai Biti na tsare kurkuku, sannan magoyan bayanmu na cikin azaba, domin an kashe a ƙalla mutane 86 daga cikin su, dubbunai sun ji raunuka, kokuma sun yi asara gidajen su saboda haka, batun hawa tebrin shawara bai taso ba."

Bisa dukkan alamu dai, taron na SADC a ƙasar Swaziland  ba zai haifar  da wani abun a zo a gani ba, ta fannin warware rikici ƙasar Zimbabwe.

Bayan sanarwar MDC ta ƙauracewa tebrin shawa, shima shugaba Tabon Mbeki yace ba za shi halaratar taron ba.

Saidai shugabanin ƙasashenTanzaniya, Angola, da na Swaziland mai masaukin baƙi na halartar taron a matsayin su na membobin komitin ƙasashe ukku mai kulla da al´amuran da suka jiɓanci siyasa da tsaro a Ƙungiyar SADC.

 • Kwanan wata 25.06.2008
 • Mawallafi Stäcker, Claus, Johannesburg (SWR)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/EQW0
 • Kwanan wata 25.06.2008
 • Mawallafi Stäcker, Claus, Johannesburg (SWR)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/EQW0