Sabuwar takaddama tsakanin kasashen Koriya | Labarai | DW | 15.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar takaddama tsakanin kasashen Koriya

Koriya ta Kudu ta yi kashedi ga takwararta ta arewa a game da wani shiri nata na neman yin gwajin wani makami mai lizzami.

Koriya ta Kudu ta yi kashedi ga takwararta ta arewa a game da wani shiri da ta ke yi na neman harba wani tauraren dan adam zuwa falaki. Kakakin ofishin ministan tsaro na Koriya ta kudun Kim Min-Seok ya ce Koriya ta arewar na neman fakewa ne kawai da wannan hujja ta harba tauraren dan Adam domin aiwatar da gwajin makami mai lizzami wanda ya saba wa yarjejeniyar zaman lafiyarsu da kuma ke a matsayin wata takula ga kasar tasa.

Ministan Koriya ta kudun ya kuma ce idan Koriya ta Arewan ta kuskura ta harba makamin to kwa za ta fuskanci sabbin takunkumai daga Majalissar Dindkin Duniya, sannan abun zai lalata batun wani taro da kasashen biyu ke shirin gudanarwa kan batun bai wa iyallan kasashen biyu da ke rabe tun a shekara ta 1953 damar saduwa da junansu.