Sabuwar majalisar ministoci a kasar Guinea | Labarai | DW | 05.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar majalisar ministoci a kasar Guinea

Majalisar ministocin Guinea da aka sanar da Yammacin ranar Litinin, ta kumshi akasari sabin membobi cikinsu kuwa mata da dama da suka samu manya-manyan mukammai.

Alpha Conde

Alpha Conde

Sabuwar Ministar kula da tattalin arzikin kasar Malado Kaba 'yar shekaru 44 da haihuwa, ta kwashe mafi yawan lokutan ayyukanta a sashen kula da cigaban kasashe na kwamitin Tarayyar Turai, yayin da takwararta ta harkokin waje Makale Kamara, ita kuma ta taba rike mukamin ministar harkokin noma a lokacin mulkin soja na Lansana Conte daga shekarar 1984 zuwa 2008 kuma ta kasance jakadiyar kasar ta Guinea a Faransa da Senegal.

Sai dai duk da arzikin karkashin kasa da Guinea ke da shi, mafi yawan 'yan kasar na cikin mawuyacin halin talauci a wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya.