Sabuwar hulda tsakanin Amirka da Cuba | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar hulda tsakanin Amirka da Cuba

Kasashen Amirka da Cuba sun tabbatar da hakan lokacin wani biki da suka shirya a ofishin jakadancin kasar Cuba a Amirka da ke birnin Washington

Kasashen Amirka da Cuba sun sake maido da huldar diplomasiyarsu bayan shekaru 54 na zaman doya da manja a tsakaninsu. Kasashen biyu sun tabbatar da hakan a ranar Litanin din nan inda suka gudanar da wani biki a birnin Washington wanda ya samu halartar ministan harakokin wajen kasar ta Cuba Bruno Rodriguez da kuma mataimakin sakataren harakokin wajen kasar Amirkan Roberta Jacobson wadanda suka jagoranci tawagogin kasashen biyu a gurin wannan biki wanda ya samu halartar sama da mutune 500.

Tuni dai aka sanya tutar kasar ta Cuba a ofishin jakadancin kasar ta Cuba a birnin Washington.Sai dai sai a watan gobena Agusta ne za a hauda tutar kasar Amirka din a ofishin jadancin kasar a birnin Havana lokacin ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Amirkan John Kerry zai kai a kasar ta Cuba.