Sabuwar gwamnati a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 22.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar gwamnati a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Bayan da aka shafe makwanni biyu ana jira, sabon firaminista Mahamat kamoun ya girka sabuwar gwamnati a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sabon firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Mahamat Kamoun ya bayyana sabuwar gwamnatin da ya girka, a wani yunkuri na daidaita kasar da yaki ya daidaita, kuma wannan na zuwa ne makonni biyu bayan da aka tilastawa gwamnatin ta sauka.

Sabuwar gwamnatin ta Kamound wadda ta kunshi mutane 31 na da sabbin mutane 19, yawancin wadanda suka kasance wakilan kungiyoyin 'yan tawaye ne bisa bayyanan da wani gidan rediyo mai suna Ndeke Luka ya bayar.

Kamoun mai shekaru 53 wanda ya kasance daya daga cikin jagororin kungiyar Seleka, ya zama firaminista ne a ran 10 ga watan Ogosta bayan da shugaba Catherine Samba-Panza ta zabe shi a wani mataki na ganin an girka gwamnatin hadakar da za ta yi la'akari da kowa da kowa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe