Sabuwar dokar fansho a Najeriya | Siyasa | DW | 02.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar dokar fansho a Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shi ne ya rataɓa hannu a kan dokar wacce ta samar da ɗaurin shekaru 10 a gidan yari ga duk mutumin da aka samu da laifin satar kuɗaden 'yan fansho.

Wannan sabuwar doka da shugaban Najeriyar ya rataɓa wa hannu wacce ta maye gurbin wacce ake da ita, da ke da nufin kare kuɗaɗen ‘yan fansho daga masu halin ɓera da satar da suke yi a tsakar rana ta kai su ga afkawa kuɗaɗen ‘yan fansho a Najeriya a yanayin da ba'a taɓa gani ba a tarihin ƙasar ,ta samu karɓuwa.

Addadin 'yan fansho waɗanda aka sace kuɗaɗensu a Najeriya ya zarta biliyan 180

Domin kuwa sannu a hankali lisafi ya fara suɓucewa a kan zahirin addadin kuɗaɗen ‘yan fansho da aka sace, waɗanda ake hasashen cewar sun zarta bilyan 180 a yanayin da ke jefa rayuwar ‘yan fansho cikin hali na mabarata a ƙasar. Duk da ma cewar sabuwar dokar ta tanadi hukunci ɗaurin shkerau 10 a gidan yari ga duk wanda aka samu ya taɓa kuɗaɗen fansho a ƙasar amma ga Alhaji Ali Abacha shugaban ƙungiyar masu karɓar fanso a Najeriyar da suka daɗe suna fafutukar sanya hukunci mai tsanani ya ce har yanzu fa da sauran aiki.

‘'To an dai yi rawar gani amma har yanzu mu dai ba mu gamsu ba, yakamata a yi irin na ƙasar China inda idan ka sace biliyoyin kuɗaɗe masu yawa za a iya yankema hukuncin kisa.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin