Sabon yunkurin warware rikicin Mali
December 20, 2012Jami'an diflomasiyya sun sanar da cewar a wannan Alhamis ne kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai jefa kuri'ar amincewa da kudirin da zai bada damar tura dakarun kungiyar tarayyar Afirka zuwa kasar Mali domin shirya kaddamar da hari akan mayakan da ke da alaka da kungiyar AlQa'ida. Dama da yammacin Larabar nan ce Faransa za ta tura tsarin kalmomin da ta ke son a yi anfani da su wajen tsara dafarin, zuwa ga mambobi 14 na kwamitin sulhun.
Kasar ta Faransa dai ta yi tsawon makonni tana tattaunawa tare da jami'an Amirka akan batun. Sai dai jami'an diflomasiyyar Amirka sun nuna ta'ba'ba game da ko rundunar da tarayyar Afirka ke shirin turawa zuwa kasar ta Mali za ta sami karfin yaki, da kuma yin galaba akan mayakan AQIM da ke zama reshen AlQa'ida ne a yankin Maghrib, da kuma na kungiyar MUJAO da ke fafutukar kaddamar da jihadi a yankin yammacin Afirka.
Idan za'a iya tunawa dai tun cikin watan Maris ne mayakan suka kwace iko da yankin arewacin kasar ta Mali, yankin da kuma fadin sa ke zama rabin kasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu