1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunƙurin warware halin ƙunci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

December 6, 2013

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta tsinci kanta cikin wadi na tsaka mai wuya tun bayan hamɓarar da gwamnatin Francois Bozize daga kujerar mulki, amma MƊD ta ɗauki mataki mai ƙwari

https://p.dw.com/p/1ATJv
UN-Sicherheitsrat Resolution zu Syrien Chemiewaffen 27.09.2013
Hoto: Reuters

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin kara yawan sojojin Faransa da na Afirka zuwa jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin kare fararen hula daga rikicin kabilanci da addini da ya ritsa da kasar.

Kudurin ya amince da tura sojojin kasashe a karkashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Afirka na tsawon shekara guda. Sojojin da aka amincewa daukar dukkan matakan da suka dace na kare rayukan fararen hula, tare da mayar da zaman lafiya da doka da oda. Dangane da wannan kudiri ne dai, ake sa ran kara yawan dakarun hadaka na Kungiyar Tarayyar Afirka da ake kira MISCA, daga 2,500 zuwa 3,500. Kazalika an amincewa sojojin Faransa za su tallafa wa sojojin Afirkan wajen tabbatar da tsaro a kasar ta ko wace hanya.

Tun daga farkon wannan mako dai, kimanin mutane 100 sun mutu cikin rikicin mai nasaba da addini a kasar ta Afirka ta Tsakiya. Rikicin kasar ya kazance ne bayan 'yan tawayen Seleka, galibi Musulmai karkashin shugaba na wucin gadi Michel Djotodia sun kifar da gwamnatin François Bozizé cikin watan Maris.

Dakaru fiye da dubu daga Faransa

Tuni dai Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka ta tura da dakaru fiye da dubu birnin Bangui, domin yin aiki kafada da kafada da rundunar MISCA ta Kungiyar Gamayyar Afirka. Hasali ma dai kudirin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ne zai baiwa sojojin damar rikidewa i zuwa dakarun kiyaye zaman lafiya. Ko da shi ma Thierry Vircoulon, shugaban yanki Tsakiyar Afirka na cibiyar International Crisis Group, sai da ya ce akwai bukatar gaggauta daukan matakai domin ceto Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daga mummunan halin da ta shiga.

Französischer Soldat in Bangui 23.11.2013
Sojojin fiye da 1000 Faransa ta tura BanguiHoto: Reuters

"Hali na gaba kura baya siyaki aka shiga a Bangui, inda a kowani lokaci daga yanzu komai na iya tayar da wutar rikici. A yanzu haka ma dai kasar ta na cikin rudu."

Rikicin ya rikide i zuwa na addini

Idan dai za a iya tunawa hambarar da Francois Bozizie da kungiyar Tawaye ta Seleka ta yi a watan Maris ne ummal aba'isan rikicin da Jamhuriyar Afirka ta samu kanta a ciki. Sai dai duk da cewa sabon shugaba Michel Djotodia ya rusa wannan kungiya daga bisani, amma kuma bai hana 'yayanta cin karensu ba tare da babbaka ba. Hasali ma dai sun 'yan tawayen wadanda galibinsu musulmi ne sun ta kai wa kiristocin kasar hare-hare, bisa zarginsu da marawa hanbararen shugaba Bozize baya. Sai dai daga bisani su ma sun kafa kwamitocin kwacar wa kansu hakki inda suka fara mayar wa musulmin da martani. Lamarin ya sa fadan daukar wani sabon salo a rikicin addini. a cewar Vircoulon na International Crisis Group.

Kasashen Faransa da Amirka sun nuna fargaba game da abin da suka kira kisan kiyashi da za a iya aikatawa a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya. Sai dai Mego Terzian, shugaban kungiyar Medecins Sans Frontieres na Faransa ya ce rikici bai kai a yaba ba.

"Akwai hare-hare da dama da ake kaddamarwa a nan da can musamman ma a Arewaci da kuma yankin Tsakiyar kasar inda rikicin ya fi kamari. Tabbas wannan ya haddasa rikici tsakanin kabilu. Amma ba na jin cewa ya kamata a danganta shi da kisan kare dangi."

Kokawa game da tabarbarewar tsaro

Sai dai Terzian ya nunar da cewa adadin sojojin da Faransa ta tura Afirka ta Tsakiya sun yi kada idan aka kwatanta da halin da ake ciki. Hakazalika ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su taimaka wa gwamnatin Afirka ta Tsakiya gudanar da ayyukan raya kasa tare da nakaltar da ita makamar shugabanci na gari.

Zentralafrikanische Republik November 2013
al'uma na fargabar kisan kare dangi a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

Da yawa daga cikin kungiyoyin agaji sun fice daga yankunan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da rikici ya fi kamari a cikinsu saboda kare rayukan ma'aikatansu. Su ma dai 'yan kasar da dama sun kaurace wa matsugunansu domin su tsira da rayukansu. Tuni ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasar na cikin barazanar fadawa cikin ja'ibar yunwa: fiye da mutane miliyan daya ne ba sa iya samun na sawa a bakin salati so uku a rana a kasar, ma'ana kashi daya bisa uku na al'umar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi: Lina Hoffmann / Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu Waba