Sabon fasali na aiki a jami'ion Benin
October 30, 2018A karkashin wata ayar doka ce da ta dauka yau da 'yan makonni, gwamnatin kasar ta Benin ta maido da hurumin zaben shugabannin jami'o'in gwamnatin a karkashinta bayan da aka kwashe shekaru 12 wannan hurumi na a hannun malaman jami'ar. A shekara ta 2006 bayan wani takun saka na tsawon lokaci da gwamnati, jami'o'in gwamnatin kasar ta Benin suka yi nasarar kwato wa kansu 'yanci na iya zaben shugabannin jami'o'in a tsakaninsu ta hanyar gudanar da zabe.
Gwamnatin Benin ta karbe hurumin nada shugabanin jami'a
Hukumomin na Benin sun dauki matakin sake karbe wannan 'yancin daga hannun malaman jami'ar suna masu bayar da hujjar cewa kwamitin zartarwa na jami'ar bai tafiyar da aikinsa ba daidai yada aka tsara kuma ma sannu a hankali ragamar jami'o'in na kubucewa gwamnatin inda ta kai ba ta sanin girman bukatun jami'o'in kasar. Matakin gwamnatin ya zo ne a daidai lokacin da malaman jami'o'in ke sirye-shiryen gudanar da zabukan wakilansu. A kan haka ne Djimon Marcel Zannou mataimakin shugaban jami'ar Abomey-Calavi ya mayar da martani.
Ya ce: ''Umurni sun zo mana daga koli cewa mu dakata a daidai lokacin da muke shirye-shiryen gudanar da zaben sabunta shugabannin jami'o'in. A yanzu ba mu da wani zabi za mu yi biyayya ga wadannan umurni za mu dakata mu ji abin da zai biyo baya"
Yanzu dai malaman jami'o'in gwamnatin na Benin sun zura ido su ga sabon tsarin da gwamnatin za ta fito da shi wajen zaben shugabannin jami'o'in. Kafin nan shugabannin jami'o'in wanda wa'adin shugabancinsu ke kawo karshe za su ci gaba da zama kan mukamansu da tafiyar da aiki.