1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kalubalen da ke gaban zababben shugaban Senegal

April 1, 2024

Kalubalen da ke gaban zababben shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye wanda zai dauki madafun iko daga hannun shugaba mai barin gado Macky Sall a wannan kasa da ke yankin Afirma ta Yamma.

https://p.dw.com/p/4eJbA
Sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar Snegal
Sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar SnegalHoto: Luc Gnago/REUTERS

Ana shirye-shiryen rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe babban zaben kasar a wani yanayi na guguwar sauyi. Ana dai ganin akwai jan aiki a gaban sabon shugaban inda ake tsamannin zai tunkari kalubale da dama.

Karin Bayani: Senegal: A hukumance an tabbatar da zababben shugaban kasa

Sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar Snegal
Sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar SnegalHoto: Luc Gnago/REUTERS

A jawabinsa na farko bayan samun nasara a zaben da ya kasance zakaran gwajin dafi, shugaba Faye bayyana cewa abubuwan da gwamnatinsa za ta saka a gaba su ne, magance tsadar rayuwa da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da sulhunta kasar. Duk da irin tashe-tashen hankulan da aka kwashe tsawon shekaru uku ana yi a kasar, matakin farko da ya dauka shi ne sasantawa da shugaban kasar mai barin gado Macky Sall a ranar Alhamis din da ta gabata, kwanaki bayan da Shugaba Fayen ya shaki iskar 'yanci.

Ga masana tattalin arziki irin su Mame Mor Sene na jami'ar Dakar, ya na ganin babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban kasar shi ne samar da guraben ayyukan yi. Alkalumman hukumomi sun bayyana cewa kashi 20 na 'yan kasar na fama da rashin aikin yi inda kuma kashi 75 na yawan al'ummar kasar miliyan 18 matasa ne.

Magoya bayan sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar Snegal
Magoya bayan sabon Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar SnegalHoto: John Wessels/AFP

Matasa ne dai dama ke kokarin tsere wa talauci daga kasar da nufin tsallakawa nahiyar Turai domin neman rayuwa mai inganci. Sene ya kara da cewa, magance wannan matsalar za ta dau lokaci kuma ba abu bane mai sauki. Sene kuma na ganin cewa, akwai jan aiki a gaban shugaba Faye na samar da yanayi mai kyau da ma dawo da kwarin gwiwar a tsakanin 'yan kasar wanda aka rasa a lokacin gwamnatin shugaba Sall.

A yanzu dai zabi ya rage wa Faye kan rusa majalisar dokokin kasar da aka kafa a shekarar 2022, wanda jam'iyyarsa ba ta da rinjaye.