1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Senegal Diomaye Faye ya nada Sonko firaminista

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ATB
April 3, 2024

Babban sakataren fadar shugaban kasar Oumar Samba Ba ne ya sanar da nadin, ta gidan talabijin din kasar, sa'o'i kalilan bayan kammala bikin rantsuwar a birnin Dakar.

https://p.dw.com/p/4eN9w
Hoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya nada babban jagoransa Ousmane Sonko a matsayin sabon firaministan kasar, bayan karbar rantsuwar kama aiki a ranar Talata.

Karin bayani:Senegal:Bassirou Diomaye Faye zai karbi mulki daga hannun Macky Sall

Babban sakataren fadar shugaban kasar Oumar Samba Ba ne ya sanar da nadin, ta gidan talabijin din kasar, sa'o'i kalilan bayan kammala bikin rantsuwar a birnin Dakar.

Karin bayani:AU ta yi fatan nasara ga gwamnatin Diomaye na Senegal

Ousmane Sonko dai shi ne dan takarar shugabancin kasar kuma jagoran adawa da gwamnatin da ta gabata ta Macky Sall, to sai dai kotun kasar ta haramta masa tsayawa takara har ma ta daure shi bisa zargin bata sunan gwamnati, daga nan ne ya dora Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon dan takara, har kuma ya lashe zaben, kwanaki kalilan bayan fitowa daga kurkuku.