Sabon shugaban kasa a Somaliya | Siyasa | DW | 08.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon shugaban kasa a Somaliya

Tsohon Firaministan Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo ya zama sabon shugaban kasar, a yayin zaben da majalisar dokokin kasar ta gudanar.

Sabon zababben shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo

Sabon zababben shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo

An zabi tsohon Firaministan Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo a matsayin sabon shugaban kasa, a yayin zaben da majalisar dokokin kasar ta gudanar. Rahotanni sun nunar da cewa tuni shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud wanda a zage na farko ya samu rinjaye kafin zaben ya sauya akala a zagaye na biyu, ya amince da shan kaye. Farmajo ya samu nasarar ne bayan da aka gudanar da zagaye na biyu a zaben, bayan da aka rasa wanda ya samu nasara a tsakaninsa da shugaba mai ci Hassan Sheikh Mohamud a zagaye na farko. Kamfanin dillancin labaran Reuters dai ya ce anjiyo harbe-harben bindiga a daf da fara zagaye na biyu na zaben.

 

Sauti da bidiyo akan labarin