Sabon shugaban hukumar WHO ya kama aiki | Labarai | DW | 01.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon shugaban hukumar WHO ya kama aiki

A wannan Asabar din ce sabon shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko kuma OMS Tedros Adhanom Ghebreyesus ya karbi ragamar jagorancin hukumar.

Tedros Adhanom Ghebreyesus Außenminister Äthiopien (Getty Images/AFP/F. Coffrini)

Sabon shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO ko kuma OMS dan kasar Habasha Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ko kuma OMS dan kasar Habasha ya zama dan Afirka na farko da zai shugabancin wannan babbar ma'aikata. Mai shekaru 52 da haihuwa kuma kwararre a fannin yaki da cutar Maleriya ya canji 'yar kasar China Margaret Chan wadda ta jagoranci hukumar ta WHO na tsawon shekaru fiye da goma tun daga ranar daya ga watan Janairu na 2007.

Kafin dai zabensa a matsayin wannan mukami na shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros ya kasance ministan harkokin wajen kasar shi ta Habasha daga shekara ta 2012 zuwa 2016 sannan ya rike mukamin ministan kiwon lafiya daga 2005 zuwa 2012. A ranar 23 ga watan Mayu ne na wannan shekara ta 2017 aka zabe shi a matsayin shugaban WHO.