Sabon shugaban babban bankin Vatican
February 15, 2013Bayan badakalar da tayi awon gaba da tsohon mai rike da mukamin gwamnan babban bankin Vatican, a wannan Jumma'ar ce fafaroma Benedict na 16- mai barin gado ya amince da nadin Ernst von Freyberg, ƙwararren lauya kuma dan kasar Jamus a matsayin sabon shugaban babban bankin na Vatican.
Wannan lamarin dai ya kawo karshen tsawon watanni tara da aka dauka na kyale mukamin - ba tare da wanda ke kula da shi ba, bayan mutumin da ya gada mukamin, ya fuskanci sallama, ba zato ba tsammani sakamakon cece-kuce akan rashin mutunta ƙa'idojin da aka tanadar wajen kashe kudi a bankin.
Wata sanarwar da ta fito daga fadar fafaroma a Vatican, ta ce hukumar kula da harkokin manyan limaman maja'miar ta fadar Vatican, wadda ke sanya ido akan lamuran bankin domin gudanar da harkokin addini, ta yi na'am da nadin shi Ernst von Freyberg a matsayin sabon gwamnan babban bankin.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar