1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinci

Matasa sun kirkiro sabon salon sayar da abinci a Senegal

Abdoulaye Mamane Amadou SB)(MAB
May 11, 2022

Wasu matasa a unguwar Linjiyan da ke yankin Ziguinchor a kudancin kasar Senegal sun kirkiro wani gidan sayar da abinci na karba ka wuce, duba da matsalolin karancin wuraren shakatawa da unguwar take da su.

https://p.dw.com/p/4B83X
Griechischer Salat
Hoto: Maksim Lashcheuski/Zoonar/picture alliance

Duk da dumbin matasa masu jin jini a jika da Allah ya albarkaci unguwar Linjiya da ke wajen birnin Ziguinchor da su, akwai kamfar wuraren sakewa da na shakatawa ga matasa. Ta wannan dalilin ne ma yasa wasu rukunin matasan masu dogon tunani suka yi nazarin kirkira sabon wurin cin abinci na zamani, a wani mataki na ba wa manyan gobe damar sakewa da hana fita.

Wannan yankuri dai ya samu nasara ga rugunin matasan hudu da suka bayan da suka jajirce wajen tabbatar da masana'antun suka samu karbuwa ga 'yan uwansu matasa. Hakan dai ya basu damar yin aikin da zai sa su yi dogaro da kai maimakon jiran biyan wata bukatarsu daga gwamnati in ji Souleymane Martiale Niouky.

Da haka da hakan dai matasan hudu sun kafa wannan kamfani kuma sun jajrice da ganin cewa komai na tafiya, bayan da suka rarraba wa kansu aikin da kowane zai iya lura da shi. Kana kuma burinsu shi ne na ganin sun bai wa wasu matasa da dama aiki a cewar Faty daya daga cikin matasa.

Ko baya ga kayan abinci matasan ka harhada kayan tande tande da na shaye-shaye irin na ji da fada wanda kuma hakan ke ba su 'yan kudaden shiga don rufa wa kansu a siri. Wannan dai ya kuma sa  da dama daga ciki matasan Ziguinchor da ba sa da aikin yi, ke marmarin kafa wasu masana'antu irin wannan a wani yunkuri na samun hanyoyin dogaro da kai.