Sabon salo a siyasar Tarayyar Najeriya | Siyasa | DW | 19.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon salo a siyasar Tarayyar Najeriya

A wani yanayi na kokarin daukar sabon salon siyasa a cikin rikicin yaki da ta'addanci a Tarrayar Najeriya, jam'iyyar PDP ta ce wasu na kokarin ganin bayan Shugaba Jonathan.

Kakakin jami'iyyar ta PDP Oliseh Metuh ne ya bayyana hakan inda ya ce ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasar ne domin kokarin ganin bayan shugaban kasar mai ci Goodluck Ebele Jonathan ko ta halin kakaka. Ya kara da cewa yakin kasar dake sauya salo da daukar hankali dai na da ruwa da tsaki da kokarin 'yan adawar arewacin Tarayyar Najeriyan na ganin karshen mulkin shugaban kasar. A fadar Metuh PDP ta damu da yadda ake zubar da jini a kasar saboda kawai ana neman kawo karshen gwamnatin 'yan tsirarun kudancin kasar ta farkon fari. Duk da cewar dai ta'addanci na matsayin annobar dake zaman ruwan dare gama duniya yanayin abun dake faruwa cikin kasar da kuma jeri na bukatu dama dodon bangon da ake yi na nuna alamun da biyu ga masu fakewa a cikin rikicin wajen neman cika buri na kare gwamnatin kasar da Jonathan ke jagoranta.

Sabuwar sanarwar da tazo dai dai lokacin da kasar ke matukar neman sulhu da sassanta dai daga dukkan alamu ta kama hanyar tada hankula harma a cikin gidan na wadata inda yanzu haka 'yan majalisar zartarwar jami'iyyar ke can ke taron kallon tasirin katobarar, da daga dukkan alamu bata da yawun abokan takun na Metuh cikin PDP.

Unruhe und Gewalt in Nigeria ARCHIVBILD

Jami'an tsaro na sintiri a arewacin Najeriya

Martani daga 'yan PDP

Ko bayan nan dai su kansu ragowar 'yan PDP a arewa maso gabas din dake fuskantar rikicin na kallon kokarin nunin yatsar jami'iyyar ya zuwa yankin nasu a matsayin kokari na tabbatar da kau da kai ga gazawar mahukuntan da dabaru ke neman karewa, a cewar Dr Umar Ardo dake zaman jigon jami'iyyar a jihar Adamawa.

"A kwai 'yan sanda a jihar Adamawa a kwai SSS a Adamawa a kwai Immigration a Adamawa a kwai kwastam a Adamawa a kwai soja a Adamawa a kwai NIA a Adamawa wadannan sune idanu da kunnuwan gwamnati, in a kwai manyan arewa suna da kunne da idanuwa a ko'ina ne, wannan magana ce ta banza, suna so suyi siyasa ne da wannan saboda gwamnati ta kasa. Tabbas gwamnati ta kasa kuma maganar tsayawar Jonathan a jami'iyar PDP ba zai yiwu ba karya ce".

Kokari na siyasa da batun rikici ko kuma neman murde wuya da nufin cika buri na shekara ta 2015 dai, tun bayan zaben shekara ta 2011 aka fara nuna alamun rabuwar gari a tsakanin dattawan na arewa da suke zargin shugaban kasar da danne damarsu ta mulki na shekaru takwas. Abun kuma da yanzu haka kakakin jami'iyar ke nunawa a matsayin tabbataci na hannun dattawan na arewa cikin rikicin da yanzu haka ya kai ga gwamnonin arewacin kasar 13 ya zuwa Amurka domin neman dauki.

Alkawarin mai da mulki arewa

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar

Jagororin jam'iyyar adawa ta APC Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar

Metuh dai ya kira ta'azzarar rikicin a sassa daban-daban na arewan a matsayin cika alkawarin dattawan na arewa na tabbatar da gazawar mulkin shugaban kasar ko ta halin kaka. Zargin kuma da a cewar Bello Sabo Abdulkadir dake zaman sakataren kwamitin dattawan arewacin kasar da yai tsayin dakan neman komawar mulkin ya zuwa arewa ke zaman zancen banza daga bakin 'ya'yan banza a cikin PDP.

"Bombing na farko da aka fara yi a kasar nan shugaban kasa da kansa yace ya san wadanda suka yi ba MEND bane, daga baya mai bashi shawara kan harkar tsaro ya fito yace PDP itace ummul'aba'isin Boko Haram. Sannan shugaban kasar da kansa ya fito yace a kwai Boko Haram a gwamnatinsa. Ai wannan zancen banza ne ai PDP ita ce Boko Haram yanzu dai suna kame-kame ne kawai na hanyar tura wa wani kashin kaji ba don basu san inda matsalar take ba".

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabuwar siyasar mai hatsari dake kara rabon 'yan kasar gida-gida tare da yin gagarumar illa ga demokaradiyyar dake fama da talauci da rashin aikin yi ko bayan rikicin na tsaro da yai mata katutu.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal/ LMJ