Sabon rikicin siyasa a Italiya | Labarai | DW | 29.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikicin siyasa a Italiya

Daya daga cikin jam'iyyun kawancen ta fice daga cikin gwamnatin kasar Italiya ta hadin gwiwa. Sai dai firaminista ya fara zawarcin wasu jam'iyyu domin kafa sabuwar gwamnati.

Firaministan kasar Italiya Enrico Letta ya fara neman goyon bayan wasu jam'iyyu cikin majalisar dokokin kasar, bayan da jam'iyyar tsohon Firamnista Silvio Berlusconi ta janye daga cikin gwamnati kawance. Samun wannan goyon baya na da muhimmanci domin kaucewa kiran sabon zabe. Shugaba Giorgio Napolitano ya nuna yiwuwar shiga tsakani saboda ganin gwamnatin ta kai labari.

Watanni bakwai da suka gabata ne aka gudanar da zaben kasar ta Italiya, kuma yanzu haka Firaminista Enrico Letta ya na bukatar tsallake kuri'ar yanke kauna da zai fuskanta a majalisar dokoki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe