Sabon rikicin addini a Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya ya barke: | Labarai | DW | 27.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikicin addini a Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya ya barke:

Jami'an lafiyar birnin Bangui na kasar suka ce tuni aka fara kulawa mutane 80 din da suka sami raunuka a asibiti a yayin da 36 suka rigamu gidan gaskiya.

Mai magana da yawun wata tawagar musulmai a yankin da rikicin ya faru Osmane Abakar yace, yamutsin ya kaure ne bayan gano wata gawa ta musulmi da ya mutu a wani masallaci dake a bangaren Kristocin, wanda hakan ya harzuka musulmin kai wani hari akan kristocin yankin a ranar a sabar.

Suma daga bisani Kristocin suka mayar da martani a ranar lahadin nan da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Jami'an lafiyar birnin Bangui na kasar suka ce tuni aka fara kulawa mutane 80 din da suka sami raunuka a asibiti a yayin da 36 suka rigamu gidan gaskiya.

Tuni dai mahukuntan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar dake fuskantar tashe -tashen hankulan addini ta ayyana dokar tabaci a yankin da al'amarin ya faru.