Sabon rikici a gabashin Kongo | Labarai | DW | 15.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici a gabashin Kongo

Kasashen Ruwanda da Jamhuriyar Dimokardiyyar Kongo na nuna wa juna yatsa dangane da sabon rikicin da ya barke a gabashin Kongo.

Wani sabon rikici ya barke a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, bayan da aka fara gwabza fada tun a jiya Lahadi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan kungiyar 'yan tawaye ta M23.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane kimanin 100 dauke da makamai daga kasar Ruwanda sun yi basaja ta hanyar yin shigar mata, tare da kutsa kai kasar ta Kongo wanda hakan'ne ya janyo sabon tashin hankalin.

A baya-bayan nan dai kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya sun zargi sojojin kasar Ruwanda da marawa 'yan tawayen M23 baya, zargin da Ruwandan ta musanta.

Sai dai har kawo yanzu kasashen biyu na zargin juna da sake rura wutar rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongon da 'yan tawayen na M23 da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dama.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe