Sabon ofishin yaƙi da Ebola a Afirka
September 20, 2014Talla
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya za ta buɗe ofishin yaƙi da cutar Ebola a yammacin Afirka wanda zai kasance a Accra babban binrin ƙasar Ghana, amma za su buɗe rassa a ƙasashen Laberiya, Saliyo da Gini. Sakatare janar na MDD Ban Ki-Moon, ya ce rashin fahimtar yanayin da ake kamuwa da cutar ya hana ɗaukar matakin daƙile annobar da yanzu ta hallaka mutane sama da 2600. Dubban jami'an kiwon lafiya a ƙasar Saliyo na ci gaba da binciken gida-gida domin zaƙulo waɗanda suka kamu da cutar ta Ebola.