Sabon kundin tsarin mulki a Tunisiya | Labarai | DW | 04.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon kundin tsarin mulki a Tunisiya

Gwamnatin ƙasar Tunisiya da ke fama da tashin hankali, ta amince da dokokin da hukuma za su riƙa aiki da su.

'Yan majalisar dokokin ƙasar Tunisiya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da maida ƙasar a matsayin Jamhuriya ta Musulunci, da ke bin tsarin addinin Islama, amma sun ƙi sa tilas a yi amfani da dokokin Alƙur'ani mai girma, a matsayin dokokin ƙasa. Ƙudurin 'yan majalisa ya ce, Tunisiya ƙasa ce mai 'yancin kai, Jamhuriyar Musulunci. Larabci shi ne harshen da za a riƙa amfani da shi a ayyukan gwamnati, kuma wannan ƙudurin babu mai sauya shi. Ƙasar Tunisiya dai ta kasa samun walwala, tun bayan da aka kifar da gwamnatin kama-karya ta Ben Ali, biyo boren 'yan ƙasar da ya haifar da guguwar juyin-juya hali a wasu ƙasashen Larabawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal