Sabon bincike kan badakalar kudi ta ″Panama papers″ | Labarai | DW | 23.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon bincike kan badakalar kudi ta "Panama papers"

Mahukuntan kasar Panama sun sanar da gudanar da wani sabon bincike a ofishin wasu lauyoyin kamfanin Mossack Fonseca da ke a tsakiyar badakalar kudin nan da ake yi wa lakabin "Panama Papers".

Mahukuntan Kasar Panama sun sanar da gudanar da wani sabon bincike a ofishin wasu lauyoyin kamfanin Mossack Fonseca da ke a tsakiyar badakalar kudin nan da ake yi wa lakabin "Panama Papers".Babban mai shigar da kara na kasar wanda ke jagorantar wanann aiki na bincike ya ce sun gudanar da sabon binciken ne bayan da suka samu sabbin bayanai da ke nuni da cewar akwai yiwuwar samun tarin takardu na aiyyukan kamfanin na Mossack Fonseca a ofishin lauyoyin.

A lokacin wannan bincike na baya-bayan nan mahukunatn Panama sun ce sun yi nasarar samun tarin takardu da ake kyautata zaton na kamfanin ne.

Binciken farko da aka gudanar a ranar 12 ga wanann wata a cibiyar kamfanin na Mossack Fonseka, ya ba da damar bankado tarin takardu na cuwa-cuwar kudi wadanda manyan masu kudi na duniya musamman 'yan siyasa da fitattun 'yan wasa ke boyewa da nufin kin biyan kudaden harajin da suka rataya a wuyansu.