Sabinta wakilai ′yan majalisun a Yukren | Labarai | DW | 28.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabinta wakilai 'yan majalisun a Yukren

Al'umma na kaɗa ƙuria' a zaɓen yan majalisun dokoki a zaɓen wanda ake wa kallon zakaran gwanji dafi ga ƙasar da ake fama da rikicin siyasa

Ana hasashen cewa jam'iyyar da ke yin mulki ta Viktor Yanukovych ita ce za ta samu rinjaye a gaban jam'iyyar jagorar yan addawar nan Yulia Timochenko, wacce aka yanke wa hukumcin ɗaurin shekaru bakwai na zaman gidan yari saboda zargin cin hanci.

Sai dai kuma masu yin nazari akan al'ammuran yau da gobe na tunanin cewar jam'iyyar Vitali Klitschko,wani tsofon ɗan wasan danben boxe ,na iya taka muhimmiyar rawa a zaɓen wanda sama da yan kallo dubu ukku ne daga ƙasashen duniya ke hallarta sa.wanda kuma duniya baki daya ta zura ido ta ga yadda za a kwashe a wannan zabe, saboda ƙaurin sunan da ƙasar ta yi wajan shirya zaɓɓuɓuka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas