1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa

December 1, 2012

Amirka ta soki Isra'ila akan sabon yunƙurinta na gina sabbin matsugunai a yankunan Falasɗinawa.

https://p.dw.com/p/16u3s
Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu and U.S. Secretary of State Hillary Clinton deliver joint statements in Jerusalem November 20, 2012. The United States signalled on Tuesday that a Gaza truce could take days to achieve after Hamas, the Palestinian enclave's ruling Islamist militants, backed away from an assurance that it and Israel would stop exchanging fire within hours. REUTERS/Baz Ratner (JERUSALEM - Tags: POLITICS CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Isra'ila ta sanar da shirin gina sabbin gidaje dubu ukku a yankunan Falasɗinawa da take ci gaba da mamayewa a gaɓar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Qudus. Wannan sanarwar ta zo ne yini ɗaya kachal bayan da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya baiwa Falasdinu kujerar 'yar kallo a cikin zauren. Daga cikin wuraren da Isra'ila za ta yi gine-ginen dai harda yankin nan da ake yiwa lakaɓi da E1, wanda ya rarrabe tsakanin arewaci da kuma kudancin yammacin kogin Jordan. Idan har ta aiwatar da wannan kudirin dai, hakan zai rarrabe tsakanin yammacin kogin Jordan din kenan, wanda zai sa Falasdinawa su fuskanci matukar wahala wajen yin zirga-zirga daga arewaci zuwa kudancin yankin. Amirka dai ta yi suka ga Isra'ila bisa bayyana wannan shirin, tare da ambata hakan a matsayin wanda ba zai haifar da sakamako mai kyau ba a kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou