1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta dauki sabbin matakai kan Kuyba

Gazali Abdou Tasawa
June 5, 2019

Kasar Amirka ta dauki sabbin matakan karya tattalin arziki ga kasar Kuyba a bisa zargin kasancewa kanwa uwar gami wajen haddasa rigingimun da ke wakana a kasashen Latin Amirka. 

https://p.dw.com/p/3JrCH
Kreuzfahrten auf Kuba
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Nova

Sabbin matakan da Amirkar ta dauka sun tanadi haramta yin balaguro na taron dangi daga Amirka zuwa kasar ta Kuyba wanda ke zama babbar kafar samar da kudaden shiga ga gwamnatin kasar ta Kuybawacce Amirkar ke zargin shugabanninta da goyon bayan gwamnatin Nicolas Maduro a Venezuwela da Daniel Ortega na Nicaragua.

 Kazalika matakin tattalin arzikin wanda ofishin ministan baitulmalin kasar ta Amirka ne ya dauke shi, ya tanadi haramta sayar wa kasar ta Kuyba jiragen ruwa da na sama daga kasar ta Amirka. Sakataren baitumalin kasar ta Amirka Steven Mnunchin ya ce matakin nasu na da burin hana kudaden Amirka fadawa hannun sojoji da ma jami'an leken asiri da na tsaro na kasar ta Kuyba. 

Wadannan matakai dai za su yi matukar illa ga harakokin yawon buda ido a kasar ta Kuyba wacce adadin yawan Amirkawan da ke zuwa yawon buda ido cikinta ya nunka gida biyu tsakanin watan Janeru da na Aprilun shekara ta 2018.