Sabbin manufofin Amirka a nahiyar Afirka | Labarai | DW | 30.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin manufofin Amirka a nahiyar Afirka

Shugaba Obama zai bayyana sabon tsarin inganta makamashin lantarki a Afirka da kuma taron koli tsakaninsa da takwarorinsa na Afirka a jawabin da zai yi a Cap; a cewar White House.

default

Shugaba Obama da mai dakinsa Michele sun isa birnin Cap.

Shugaban Amirka Barack Obama ya isa Roben Island inda Nelson Mandela da ya yi gaggwarmayar yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu ya shafe shekaru 18 a tsare. Daga bisani ne kuma Obama zai nufi jam'iyar Cap inda zai bayyana sabbin manufofin Amirka a kasashen Afirka, a ziyararsa da ke zama ta biyu a wannan nahiya tun bayan daya hau kan kujerar mulki. Ita dai kasar ta Amirka ta na neman karfafa dangantakarda da afirka, nahiyar da China da Indiya ke ci gaba da samun angizo.

Tuni na ma dai fadar mulki ta Washington ta riga ta bayyana cewa daga cikin muhimman batutuwa da zai yi a jawabin na sa, har da batun gudanar da wani taron koli tsakaninsa da shugabannin kasashe Afirka a kasar Amirka a shekara mai zuwa . Daya daga cikin masu mai wa Obama shawara a fannin tsaro Ben Rhodes ya nunar da cewa Shugaba na Amirka zai kuma bayyana wani tsari na inganta wautar lantarki a kasashen Afirka wanda zai lakume kudi miliyan dubu bakwai na Dolla cikin shekaru biyar masu zuwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman