Sabbin hare hare a Irak | Labarai | DW | 16.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare hare a Irak

Mutane a ƙalla guda 27 suka mutu yayin da wasu 235 suka jikata a hare haren da suka zo a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali a ƙasar

Jerin hare haren da ake kaiwa a birnin Bagadaza a wasu garuruwa guda biyu na yankin arewacin ƙasar a wani hari ƙunar baki wake da wasu mutane guda biyu suka kai da wasu motocin da suka tashi da bam kusa da cibiyar wata jam'iyyar siyasa ta ƙurdawa na zaman wata sabuwar dambarwa da ta kuno kai a ƙasar.

Garuruwan guda biyu na Kirkuk da Touz Khurmatou suna daga cikin waɗanda ake yin jayaya a kan su tsakanin gwamnatin da ƙurdawa Iraki.Masu aiko da rahotannin sun ce waɗannan sabin hare hare na iya ƙara zafafa kai ruwa rana da ake yi tsakanin firaminista Iraki dan shi'a ;da masu yin adawa da shi yan sunni waɗanda a yan kwanakin baya baya nan ,suka daɗa yin zanga zanga.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Awal