Sabbin hare-hare a garuruwan Izge da Malari da ke a jihar Borno | Labarai | DW | 23.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare-hare a garuruwan Izge da Malari da ke a jihar Borno

Hare-haren waɗanda da ake zaton cewar 'yan Ƙungiyar Boko Haram ne suka kai su, a garuruwan da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya an kashe mutane da dama.

Wasu maharan da ake zaton 'yan Ƙungiyar Boko Haram ne sun kai wasu sabbin hare-hare a garuruwan Izge da Malari a jihar Borno da ke a yanki Arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya. Mazauna garin Izge da yanzu haka suka tsere sun bayyana cewar 'yan bindigar sun yi ta yin luguden wuta a garin har sai da suka tabbatar duk wani mai motsi ya ƙare tare da ƙona garin ƙurmus.

Yanzu haka dai babu kowa a garin na Izge wanda ya sha fama da hari a makon da ya gabata wanda a cikin aka samu hasarar rayuka sama da 100. 'Yan bindigar sun kai hari kuma a garin Malari mai nisan kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar inda ake da fargabar an samu hasarar rayuka da dama.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman