1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani kan amincewa da kudurin sauyi

March 25, 2014

Yukurin sauya tsarin amincewa da wani kuduri daga kashi 75 cikin 100 da gwamnati ta tsara zuwa kashi biyu bisa uku ya haifar da takaddama a taron kasa.

https://p.dw.com/p/1BVay
Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Hoto: DW/U. Musa

An dai tada jijiyar wuya ne har ma da daga murya a kan wannan batu na ka'idar da aka gindaya wajen amincewa da duk wani batun da aka kasa samun daidaito a tsakanin wakilan taron kasar su 492, inda dole a kaiga amfani da amincewa da kashi 75 na wakilan don cimma matsaya.

To sai dai wasu wakilan sun nuna adawa da wannan tsari bisa hasashen cewa ba zai samar da kyakyawan sakamako ba, don haka sai a yiwa tsarin gyara a maida shi amfani da kasha biyu bisa uku da aka saba da shi a tsarin dimukurdiiyar Najeriyar, musamman a majalisun dokoki, kuma ma wannan tsari ne aka yi amafani da shi a daukacin tarurrukan kasa makamantan wannan da aka yi a kasar. Barrista Dan Anyawu ya ce akwai dalilan da suka sanya su dagewa kan wannan matsayi.

Ya ce "wannan taro ya huta domin na gabatar da goyon baya bisa kan cewa duk batutuwan da wannan taro zai cimmawa a amince da su bisa ga kashi biyu bisa uku, duk inda aka samo akasin haka a maida shi inda ya fito."

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP Photo

Amma ga wasu wakilan sun dage kan cewa akwai fa'idar da ta sanya gwamnati sanya wannan sharadi na samun amincewar kashi 75 cikin 100 na wakilan taron kasar a kan duk wani batu saboda nauyi da ma muhimmancin batutuwan da za'a tabo, wadanda za su shafi mutane masu rinjaye ne na al'ummar Najeriyar. Farfesa Auwalu Yadudu wakili ne a taron kasar, wanda ya ce akwai fa'ida tattare da sharadin da gwamnati ta gabatar, kuma ba ma wani sabon abu ne aka gabatar ba:

"Kamata ya yi a gane cewar shi kundin tsarin mulki kullum yana tanadi na ta yaya za'a kawo canje-canje gareshi. Akwai canje-canjen da ake ganin kanana ne akwai manya, don wasu ma ai kashi hamsin cikin 100 ake bukata. Amma me yasa aka nemi wannan saboda abu ne muhimmi ba zaka yi canjinsa haka giri-giri ba, sai ka natsu sosai. Don haka wannan ba wani sabon abu ne shugaban kasa ya kawo ba."

Ja-in-jan da ake fuskanta tun ma kafin a kai ga fara tattauna muhimman batutuwa kan taron na zama abin da ke daga hankalin al'ummar kasar da dama kan taron kasar dake da karancin lokaci na tattauna batutuwa muhimmai da suka shafi kasa. Hajiya Aishatu Ismail wakiliya daga jihar Kano ta ce wannan ba abin daga hankali bane:

Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Komitin shirya taron kasaHoto: DW/U. Musa

" Ba za'a ce wai an sa wannan taron kasa kamar ba za'a gama shi ba, za'a gama shi mana, ka san cewa ba wai zaman na dakin taro kadai bane, akwai lokacin da za'a karkasa mu don mu tattauna abubuwa da yawa. Kasan yanzu farko farko ne kuma abubuwa da dumi kowa na son a ji muryarsa tukuna."

Da alamun za'a ci gaba da tada jijiyar wuya a taron kasar musamman idan aka kai ga batutuwa na rabon arzikin kasa da ke zama sandar duka ga sassan da ke ganin su ne ke da mallakarsa ba wai kasar ba.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar