Saadi Gaddafi ya shiga hannu
March 6, 2014Majalisar zartaswar kasar Libiyan a karkashin jagorancin Firaminista Ali Zaidan ce ta tabbatar da mika Saadi Gaddafin inda ta ce a yanzu haka yana gidan kaso a Libiyan bayan da ya iso daga Jamhuriyar Nijar din. Saadi, dai ya tsere ne zuwa Jamhuriyar Nijar tun bayan da aka kifar da gwamnatin babansa ta mulkin kama karya a juyin-juya halin da ya samu goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO a shakara ta 2011.
Saadi Gaddafi, baya daga cikin wadanda kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ke nema ruwa a jallo, sai dai mahukuntan kasar ta Libiya na son tuhumar Saadi da laifin almubazzaranci da kuma yin amfani da makami wajen firgita 'yan wasa a yayin da yake shugabantar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Libiyan. Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasar dai na neman a mika mata daya daga cikin 'ya'yan marigayi Gaddafin wato Saif al-Islam bisa zarginsa da aikata laifukan yaki, sai dai har kawo yanzu yana tsare a hannu tsagerun Libiyan masu dauke da makamai da suka cafke shi bayan kifar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafin.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman