Sa-in-sa tsakanin Amurkawa da masu adawa gyara dokar mallakar makamai
December 21, 2012Talla
Kungiyar ta National Rifle Association dai ta ce wannan mataki zai taimakawa kasar wajen ganin an kare rayukan Amurkawa a makarantu da sauran wurare.
Wannan kiran dai na kunshe ne cikin taron manema labarai da kungiyar ta yi, inda mataimakin shugabanta Wayne LaPierre ce kungiyar za ta taimakawa makarantu da horo dangane da yadda za su kare kansu.
Amurkawa a birnin Washington dai sun gudanar da zanga-zanga ta nuna rashin amincewarsu da wannan mataki.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman