Ruwanda: Sa ido na hukumar zabe ga shafukan sada zumunta | Labarai | DW | 01.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruwanda: Sa ido na hukumar zabe ga shafukan sada zumunta

Hukumar zaben kasar Ruwanda ta sanar da soke matakin da ta dauka na sa ido kan bayannan da 'yan takaran neman shugabancin kasar za su rinka wallafawa ta shafukan sada zumunta na Internet.

Ruanda vor den Wahlen 2017 (Imago/Zumapress/M. Brochstein)

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame

Hukumar zaben ta Ruwanda ta bakin shugabanta Kalisa Mbanda ta ce ko wane dan takara ya na iya wallafa sakonsa ta shafukan na sada zumunta, amma kuma idan ya saki hanya zai gamu da fushin doka. A 'yan kwanakin bayan nan ne dai hukumar zaben kasar ta Rwanda ta NEC ta dauki matakin wanda da farko ya kamata ya soma aiki daga ranar 14 ga watan Yuli mai zuwa, amma ya fuskanci babban kalubale daga masu kare hakin albarkacin baki da ma sauran 'yan kasar.

Shugaban hukumar zaben ta Ruwanda ya ce wannan mataki sun so su dauke shi ne domin kauce wa yada wasu kalammai da za su iya tayar da zaune tsaye, da raba kanun 'yan kasa a kasar da ta fusknaci yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 800 a shekara ta 1994.