1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rusesagabina: Shekaru 25 a gidan kaso

September 20, 2021

A ranar litinin (20.9.2021) kotu a Ruwanda ta yanke wa Paul Rusesagabina hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 25 bayan samunsa da ta yi da laifukan ta'addanci. 

https://p.dw.com/p/40a9b
Ruanda | Paul Rusesabagina | Anklage erhoben
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Rusesabagina dai na zama tsohun manajan Otel a Ruwanda da masana'antar shirya fina-finai ta Amirka wato Hollywood ta shirya fim a shekarar 2004 kan labarinsa na kare daruruwan rayuka a lokacin rikicin kisan kare dangi na Rwanda a shekarar 1994. 

Masu gabatar da kara sun bukaci kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifuka 9 sai dai mai shari'a Beatrice Mukamurenzi ta ce an masa sassauci kasancewar wannan ne karon farko da aka taba yanke masa hukunci.

Ana dai yanke Rusesabagina wanda ya shahara wajen sukan lamirin gwamnatin shugaba Paul Kigame hukuncin ne bisa samun shi da laifin kitsa wasu hare-hare a Ruwanda a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019 kana ya na taimakawa kungiyoyin tawayen kasar daga ketare.