Ruwanda: An ceto gawarwakin ′yan Kwango | Labarai | DW | 20.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruwanda: An ceto gawarwakin 'yan Kwango

A kasar Ruwanda an fito da mutanen da suka samu hadarin jirgin ruwa a lardin Kivu na kasar Kwango kwanaki bayan sun yi hatsari a cikin jirgin ruwa kan hanyarsu ta zuwa yankin Goma.

Masu ceto a gabar ruwar kasar Ruwanda sun tsamo gawarwakin wasu 'yan Jamhuriyar Demukradiyar Kwango 15 da wani jirgin ruwansu ya nutse da su a dare Litinin zuwa Talatar da ta gabata a lardin Kivu na kasar Kwango.

Tuni hukumomi a Ruwanda suka mayar da gawarwakin zuwa kasar Kwango domin yi masu jana'iza in ji wani jami'in kungiyar bayar da agajin gagawa ta Croix Rouge ko Red Cross na kasar Ruwanda.

An jima ana samun nutsewar jiragen ruwa a Kwango musamman ma a gabar Kivu da Goma bisa dalilai na rashin inganci wanda ko a baya bayan nan shugaban kasar da kansa Félix Tshisekedi ya nuna juyayi ga wasu iyalan mutane 142 da suka nutse a cikin ruwa ciki har da kananan yara.