1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruwa ya mamaye wasu unguwannin Kinshasa bayan ambaliya

Mouhamadou Awal Balarabe
October 19, 2024

Wannan shi ne ruwa mafii karfi da aka yi tun bayan saukar damina a Kinshasa mai kunshe da mutane miliyan 17, amma ba a samu asarar rai ba.

https://p.dw.com/p/4lzRi
Biranen Afirka da dama na fama da ambaliyar ruwa
Biranen Afirka da dama na fama da ambaliyar ruwaHoto: Amas Eric/DW

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata a  Kishasa ya haifar da ambaliya a wasu unguwanni na babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda kogi ya cika ya batse. Wannan dai shi ne ruwa mafii karfi da aka yi tun bayan saukar damina a Kinshasa mai kunshe da mutane miliyan 17, amma ba a samu asarar rai ba.

Karin bayani: Ambaliya ta kashe mutane a Najeriya

Sai dai a kafofin sada zumunta, an watsa bidiyoyin yadda ambaliyar ke awon gaba da manyan motoci a tsakiyar tituna. A gudnmuwar Limete da ke tsakiyar birnin Kinshsa, kududdufai da magudanar ruwa sun cika makil, yayin da ruwa ya kai kirjin wasu mazauna yankin, inda wasu suka biya majiya karfi wajen tsallakar da su.

Karin bayani: Asarar rayuka da dukiyoyi saboda ambaliya
 
 A Kinshasa dai, ruwan sama mai karfi da ke haddasa ambaliya a kai a kai na lakume rayuka da dukiyoyi, inda a watan Nuwamban  2019, kusan mutane 40 ne suka mutu a babban birnin Jamhuriyar Dimukaraduiyyar Kwango, sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa zabtarewar kasa.