Rundunar Monusco za ta janye daga Kwango
April 2, 2014Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango wato Monusco ta sanar da cewar za ta janye da sannu a hankali daga ƙasar bayan ta kwashe shekaru da dama tana aikin tabbatar da zaman lafiya. A wani taron manema labarai da ya yi a yau a birnin kinshasha, jagoran rundunar Martin Koblerdan asilin kasar Jamus, ya ce "tafiyar ba yau ba ne, ko gobe, ko jibi, ya ce zamu janye da sannu a hankali."
A cikin watan Disamba aka shirya babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon zai gabatar da ƙudirin janye rundunar. Bayan da dakarun suka yi nasara a kan ɓangarorin 'yan tawaye da dama da ke a gabashin Kwangon abin da ya sa aka samu kwanciyar hankali. Akwai dakaru kusan dubu 20 na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke jibge a ƙasar ta Kwango.
Mawallafi: Abdourrahamane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal