Rundunar JTF ta ce akwai nasara a yaƙi da Boko Haram
January 14, 2013Rundunar tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Borno wacce aka fi sani da suna JTF ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wani babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram mai suna Mohammed Zangina da aka fi sani da Mallam Abdullahi Alhaji Musa, wanda akansa rundunar ta sa kuɗi Naira miliyan 25 ga duk wanda ya kawo shi da rai ko a mace.
A cewar runudanar tabbatar da tsaro ta JTF Mohammed Zangina da aka fi sani da Mallam Abdullahi ko Alhaji Musa daya ne daga cikin manyan ‘yan majalisar koli da ake kira “Shura” ta Kungiyar gwagwarmayar, kuma yana da hannu a shirya yawancin hare-hare da aka kai a sassan kasar wanda kungiyar ta dauki alhakin kaiwa.
Kakakin rundunar ta JTF Laftanar Kanar Sagir Musa ya bayyana cewa sun samu nasarar kama shi ne a Maiduguri bayan musayar wuta da aka yi, inda ya kara da cewa a baya ya sha tsallake kwanton ɓauna da aka yi a maboyar sa a garuruwan Jos da Zaria da Potiskum da Damaturu. Kame wannan kwamandan na zuwa sa'o'i 24 bayan da jami'an tsaron suka bayyana kame wani kwamandan ƙungiyar ta Ahlul Sunnan Li'dda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko haram a gidan wani tsohon dan majalisar wakilai da ya fito daga jihar Borno.
Sai dai jama'a na bayyana shakku kan wannan kame da jami'an tsaro suka ce sun yi, don haka tambayi Isma'il Yunusa wanda aka fi sani da Malam Kaka daya daga cikin masu wannan shakku, inda ya bani dalilin sa kamar haka. A baya ma dai rundunar ta ayyana kame wasu manyan kwamnadojin yaki na wannan kungiya, amma har yanzu ba a kai ga bayyana su gaban al'umma ba, wannan a cewar Malam Ahmad Gombe da lauje cikin nadi in ba haka ba da an bayyana su.
A wata sabuwa kuma rundunar tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a jihar Borno ta sake jaddada cewa boye ‘yan kungiyar Boko Haram da al'ummar jihar Borno ke yi da kuma rashin baiwa jami'an tsaro hadin kai, shine ke zama babban kalubale ga kokarin shawo kan matsalar rikicin. Kakakin rundunar Laftanar Kanar Sagir Musa wanda ya bayyana hakan yace ya zama dole al'umma su taimaka wa jami'an tsaron in dai ana son kawo karshen wannan tashin-tashina. Saboda haka ya shawarci al'ummar jihar da su fito su bayyana inda masu kai hare-haren ta hanyar bai wa jami'an tsaro hadin kai da bayanai da za su taimaka musu a ayyukan su.
Sai dai da wuya jama'a su bada hadin kai ga jami'an tsaron bisa hujjojin da al'umma ke bayarwa na rashin kyakkyawan dangantaka tsakanin al'umma da jami'an tsaro, kamar yadda Malam Kaka da Ahmadu Gombe suka bayyana min. To amma jami'an tsaron na musanta wannan zargi da al'umma ke yi, inda suke kara karfafa gwiwar su tare da bada tabbacin rufe asirin duk wanda ya taimaka musu.
Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammad
Edita: Usman Shehu Usman