1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rukunan gasar cin kofin duniya 2022

April 1, 2022

A wannan Juma'ar an raba rukunnan gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na ta bana da za a gudanar a kasar Katar zuwa gida takwas.

https://p.dw.com/p/49MKB
Katar Doha | FIFA Fußball WM 2022 Auslosung | England
Hoto: Shaun Botterill/Getty Images

Mai masaukin baki Katar ta fada a rukuni na A wato rukuni daya da kasashen Ecuador da Senegal da kuma Netherlands. Kasar Ghana da ta fitar da Najeriya daga shiga gasar ta na rukuni na H inda za ta kece raini da kasashen Portugal da Uruguay da Koriya ta kudu.

Kasar Jamus kuwa ta fada ne a rukuni na E inda anan ma kasashen Spain da New Zealand da Japan suka fada. Ita kuwa Ingila ta fafata da kasashen Iran da Amirka da kuma Ukraine a rukuni na B. A taron raba rukunan da ya gudana a birnin Doha na kasar Katar kasar Faransa da ta lashe gasar da ta gabata ta fada a rukuni na D da kasashen Hadaddiyar daular larabawa da Denmark da kuma Tunusiya.

Za a dai a fara gudanar da gasar ne a ranar 21 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2022 a birnin Doha na kasar Katar.