Rudanin siyasa a Venezuela | Labarai | DW | 26.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rudanin siyasa a Venezuela

Majalisar dokokin kasar ta mika sammacin neman shugaban kasar Nicolas Maduro ya bayyana a gabanta bisa aikata laifuka na rashin iya mulki da yin sakaci kan mukaminsa

Majalisar kasar Venezuela ta gabatar da shugaba Nicolas Maduro a kotu, don karya ka'idojin kundin tsarin mulki. Majalisar wace 'yan adawa suka fi rinjaye, ta bukaci a caji shugaba Madora da barin mukaminsa, kana da aikata laifuka da kuma kin sauke nauyinsa a siyasance.

Wannan dai shi ne wata sabuwa rikita-rikita a kasar, da a yanzu ke cikin matsaloli bila adadin, kama daga karancin abinci, da magungunan kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Majalisar dai ta aika sammaci wa shugaba Madora da ya bayyana gabatanta a makon gobe. To amma wannan matakin zai kasance kawai na jeka na yika ne, domin majalisar dokoki a bisa tsarin mulkin kasar, bata da ikon sauke shugaban kasa.