1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga rudanin siyasa a kasar Cote d'Ivoire

Abdoulaye Mamane Amadou GAT
July 9, 2020

Mutuwar firaministan kasar Cote d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ta haifar da rudanin siyasa a kasar musamman kasancewarsa mutum,an da jam'iyya mai mulki ta RHDP ke shirin tsayarwa takara a zaben shugaban kasa na tafe.

https://p.dw.com/p/3f46d
Amadou Gon Coulibaly | Premierminister der Elfenbeinküste gestorben
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Ana ci gaba da nuna alhinin rasuwar firaministan kasar Cote d'ivoire Amadou Gon Coulibaly, wanda Allah ya yi wa cikawa a Larabar wannan mako a sakamakon bugun zuciya. Sai dai mutuwar ta Gon Coulibaly ta jefa kasar cikin wani yanayi na rudanin siyasa kasancewa shi ne mutuman da jam'iyya mai mulki ta RHDP ke shirin tsayarwa takara a zaben shugaban kasa da kasar za ta gudanar nan da watanni uku.


Shugabannin kasashen duniya ciki har da na Faransa wacce ta yi wa kasar ta Cote d'Ivoire mulkin mallaka dai na ci gaba da nuna alhini ga 'yan kasar bisa abin da ya faru na rashin dan takarar shugabancin kasar Firaminista Amadou Gon Coulibaly. Faransa ta nuna marigayi Coulibaly a matsayin babban amininta da kuma ya yi ruwa da tsaki wajen sake farfado da tattalin arzikin kasar. Ga Shugaba Emmaneul Macron na Faransa rashin Amadou Gon Coulibaly wata babbar asara ce a yayin da ake tunkarar manyan zabukan a kasar ta Cote d'Ivoire.

Wannan juyayin na zuwa ne biyo bayan wani irinsa da shugaba Allassane Ouattara ya yi tun daga farko a daren jiya, inda sanarwar fadar shugaban kasar da kakakinta Patrick Achi ya karanta ta nuna cewa Koulibaly ya taka wata muhimmiyar rawa da ka iya zama abar misali a tsakanin ma'aikatan kasar masu matsakaitan shekaru:

Elfenbeinküste Abidjan | lassane Ouattara und Amadou Gon Coulibaly
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

 "Kasar Cote d'ivoire ta yi asarar wani babban abin misali musamman ma ga matasanta, babban abin misali wajen juriya da daure wa aiki da kwarewa ta kowane fanni."

Sai dai wani batun da ya fi daukar hankali a yanzu shi ne makoma da alkiblar siyasar kasar ta Cote d'Ivoire, musamman ma ga jam'iyya mai mulki ta RHDP wadda Shugaba Allassane Ouattara ya zabar wa maragayin a matsayin wanda zai gaje shi. Sai dai a cewa Boureima Fofana wani kusa a Jam'iyyar, wannan ba wata babbar matsala ba ce:

"Ko kadan ba mu cikin wani yanayi, domin RHDP ba karamar jam'iyya ba ce, muna da tsarinmu kuma jam'iyyar za ta gudanar da taro domin sake fitowa da wani dan takarar da ka iya kai mu ga lashe zabe. A garemu ba wata matsala ya kasance ko Hamed Bakayogo ko kuwa ma ya kasance Allassane Ouatara ko wani dan takara na daban. Bukatarmu ita ce ta samun wani wanda zai yi biyayya ga jam'iyya, kana kuma duk wani zabin da Shugaba Ouattara ya yi shi ne za mu yi wa biyayya."

'Ya 'yan jam'iyyar da ke mulki dai na yi wa mutuwar firaministan kallon wani sabon babi ne da ya sake budewa a cikin harkokin tafiyar siyasar kasar. To amma a nasu bangare masu sharhi na yi wa batun kallon wani sabon babi ne na sarkakiyar siyasa ya sake budewa a kasar mai karfin tattalin arziki a jerin kasashen renon Faransa da ke yammacin Afirka. Ouattara ka iya amai ya lashe domin sake tsayawa takara ganin cewa tun daga farko ya dogara ne ga dan takarar da ya yi wa duniya bankwana a yanzu. Sai dai a cewar wani kusa a jam'iyyar hamayya ta PDCI Shugaba Ouattara ba zai yi sake ya yi wa batun hawan kaho ba:

"Kundin tsarin mulki ya takaita wa'adin har sau uku na mulkin Shugaba Ouattara, saboda hakan mu ba za mu nuna wata damuwa ba ganin cewa mun yarda da Ouattara a matsayinsa na dan dimukuradiyyar da bai yi sake ya kasa biyayya ga kundin tsarin mulki ba, domin ya bayyana hakan a cikin watan Maris da yagabata na cewa zai damka mulki a hannun matasa."


To ko yaya masu sharhi ke kallon batun da ke neman zama wata sabuwar cece-kuce ga harkokin siyasar kasar ta Cote d'ivoire?  Farfesa Ousmane Zina malami a tsangayar siyasa da ke jami'ar Bouake a kasar Cote d'ivoire cewa ya yi:

Mitglieder der Regierungspartei RDR in der Elfenbeinküste
Hoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

"A yanzu komai na iya faruwa domin Shugaba Ouattara na iya dawowa a cikin harkoki gadan-gadan. Ya'alla ko ya kama wa daya daga cikin 'yan takara ko kuwa ma ya tsaya da kansa domin duk wani tsarin da aka yi an yi shi ne kan dan takarar da ya rasu. Ba wata tababa da cewar Ouattara  da kansa zai iya dawowa duba da yadda matsalolin suka kasance a yanzu da kimarsa a cikin jam'iyyar ta RHDP maimulki".
 

A yanzu dai hankali ya koma kan 'yan takarar da suka nuna sha'awarsu tun daga farko kafin Shugaba Ouattara ya amince da Amadou Gohn Koulibaly a matsayin dan takara. Daga cikinsu akwai Hamed Bakayoko, Patrick Achi da dai sauransu. Amma kuma duba da yadda a bangaren 'yan adawa masu fafatukar neman shugabancin kasar ke da 'yan takara masu kima ciki har da Henri Konan Bédié da ya taba shugabantar kasar a baya da wuya Allassane Ouattara ya iya samu mafi kimar 'yan hamayya daga cikin jam'iyyarsa. Dan haka wasu ke ganin ba mamaki Ouattara ya tsaya takarar da kansa.