Romano Prodi ya gabatar da jerin sunayen ministocin sa
May 17, 2006Talla
FM Italiya mai jiran gado Romano Prodi ya kammala nada membobin sabuwar gwamnatinsa ta masu matsakaicin ra´ayin sauyi kuma a na sa ran rantsad da ita a wani lokaci yau laraba. Yanzu haka dai ya mikawa shugaban kasa Giorgio Napolitano jerin sunayen wakilan gwamnatin. Mukami mai muhimmanci shi ne wanda aka bawa tsohon FM Massimo D´Alema wanda aka nada shi a mukamin mimnistan harkokin waje. Yayin da Tommasi Padoa tsohon dan kwamtin zartaswan babban bankin Turai, ya samu mukamin ministan tattalin arziki. To sai dai kawance masu tsattsauran ra´ayi da kuma ´yan gurguzu sun nuna rashin jin dadinsu ga jerin sunayen wakilan gwamnatin, kuma nan gaba kadan zasu yanke shawara ko dai su ci-gaba da kasancewa cikin kawance da Prodi ko kuma su fice.