Rikicn PDP na barazana ga dorewar jam′iyyar | Siyasa | DW | 14.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicn PDP na barazana ga dorewar jam'iyyar

Sannu a hankali jam'iyyar PDP dake jan ragamar mulki a tarayyar Najeriya na kara shiga tsaka mai wuya da fuskantar makoma maras tabbas a kasar.

Ta dai gaza zaben shugaban kwamitin amintattunta shekara kusan guda da saukar tsohon shugabanta, ta ma gaza kaiwa ga kiran taron majalisar zartarwa cikin tsawon kusan watanni takwas, sannan ita kanta majalisar zartarwar tata na barazanar darewa da karancin kudin da ta dade ba ta kalli irin sa ba. Duk dai sakamakon rikici na cikin gida da ya kai iya wuya ga jam'iyyar PDP mai mulki a cikin tarrayar Najeriya da yanzu haka kuma ke barazanar gurgunta daukacin harkokin jam'iyyar.

Duk da cewar dai ta sha shiga tana fitowa a cikin karfi, a wannan karo dai daga dukkan alamu rikicin da ya raba kan daukacin gwamanonin da suka hada karfi da tsohon shugaban kasar da yaransa a gefe guda sannan kuma da fadar gwamantin kasar dake jagorantar shugabannin gidan wadata a kokari na bara'a da babakere irin na gwamnonin dai na barazanar nuna alamar kawo karshen ikon jam'iyyar da ta share shekaru 14 kan gadon sararuta yanzu haka kuma ke neman komawa ya zuwa Allah Sarki.

Kokarin dinke baraka tsakanin 'ya'yan PDP

Former Nigeria military dictator and presidential candidate for the Congress for Progressive Change (CPC) retired General Muhammadu Buhari speaks on the April elections in Lagos on March 15, 2011. Nigeria holds presidential, state and legislative elections in April in a test to see if it will break with its history of deeply flawed and violent polls. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya

Hankali dai ya tashi ga fadar Aso Rock da ta kira wani taron kungiyar G84 ta masu fada ajin jam'iyyar da kuma shugabanta Goodluck Ebele Jonathan ke kuma fatan samun goyon bayansu ga kokarin ganin bayan gwamnonin da tabbatar da iko na Jonathan kan kowa a cikin jam'iyyar.

Alhaji Isa Tafida Mafindi dai na zaman shugaban kungiyar da yace tura ta kai bango kuma hakurinsu ya kare ga yadda jam'iyyar tasu ke kara sukurkucewa a duk ranar Allah.

Razanar da tarrayar Najeriya ko kuma fadan kaiwa baki dai, babban batun na zaman na burin mulkar kasar cikin tsawon wasu shekaru biyu masu zuwa batun kuma da ya raba jam'iyyar zuwa tanti tanti gida gida sannan kuma ke barazanar mika ta ga hannun 'yan APC da suka kafa tarko kuma ke shirin kame manyan 'ya'yan ta da tuni suka fara tunanin sauyin sheka.

Barzanar canza sheka daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya

Tuni dai aka fara hasashen yiwuwar komawar da dama daga cikin gwamanonin PDP na arewa cikin APC da nufin yakar shugaban in har ya yi nasarar fin karfin kowa a cikin PDP.

Büro der Oppositionspartei Actopm Congress of Nigeria in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013

Shelkwatar jam'iyyar adawa ta ACN a Abuja

Amma dai fara ambato wasu gwamnonin na marhabin da haihuwar APC da a cewarsu za ta taka barki ga rashin adalcin PDP na lokaci mai tsawo.

To sai dai kuma a cewar Faruk BB Faruk dake zaman tsohon dan majlisar zartarwar PDP da kamar wuya ga Jonathan din ya gano keyar gwamnonin cikin gwagwarmayar da tarihinta ke tabbatar da tasirin gwamnonin cikin daukacin harkokin jam'iyyar.

Abun jira a gani dai na zaman neman mafita ga jam'iyyar ta PDP da daga dukkan alamu ta yi nisa a cikin ramin rikici sannan kuma ke matukar burin dorewa a cikin mulkin kasar ta Najeriya ya zuwa illa ma sha Allah.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin