1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Zirin Gaza

Zainab MohammedJanuary 2, 2009

Dakarun Izraela na cigaba da Kazamen hare-hare a gaza

https://p.dw.com/p/GR1Z
Hoto: AP

Jakadan Majalidar Ɗunkin Duniya Robert Serry yayi kira dangane da darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, domin kawo karshen hare-haren da Izraela ke cigaba da aiwatarwa.

Robbert Serry yayi wannan kiran ne bayan yini bakwai na kai somame zirin Gazan da jiragen yaki ta sararin samaniya da dakarun Izraila keyi. Yace tsagaita wuta ne zai samar da hanyar da za a samu daman shigarwa da palastiwana abinci da sauran kayayyakin masarufi da suke bukata.

"yace dole mu duba tsarin tsallakawa zuwa cikin gaza.Abunda muke bukata dai shine ɗorewar samun daman shigar da kayayyakin agaji"

A taron manema labaru da yayi a birnin kudus,adaidai lokacin da sojin Izraelan ke aman boma bomai a zirin Gazan, jakadan na musamman yace dole ne ɓangarorin biyu su darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Serry yace kamata yayi ɓangarorin biyu suyi koyi da kura kurensu na baya,bayan cikan wa'adin tsagaita wuta na wata shida a ranar 19 ga watan Disamban daya gabata.

Ya kumayi amfani da wannan daman wajen kira ga shugaba Mahmoud Abbas daya sake karɓan madafan iko a zirin na Gaza, tun bayan da dakaraun Hamas suka fatattaki nasa a watan yunin 2007.

CONDOLEEZZA RICE
Hoto: AP

A ɓangaren ta sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice, danganta wannan hali da ake ciki tayi da gwamnatin Hamas dake rike da madafan iko a zirin gaza.

"Tace zan fara dacewar 'yam Hamas gasawa al'ummomin gaza tsakuwa ne a hannu, tun bayan da suka kwace madafan iko daga karkashin 'yantacciyyar gwamnatin Mammoud Abbas.Tun daga wannan lokaci ne suka daɗa tsanantawa palastiwan zirin Gaza halin da suke ciki na kuncin rayuwa. Amma mu a ɓasngaremmu kokari mukeyi muga cewar an cimma tsagaita wuta a wannan rikici daya kunno kai".

Gwamnatocin ƙasashen duniya dai na cigaba da kira da bukatar tsagaita wuta, ayayinda primiyan Izraelan Ehud Olmert yake gudanar da taron manyan ministocin ƙasar.Ministan tsaro Ehud Barak da ta harkokin waje Tzipi Livni da jami'an leken asirin Izraelan ne ke halartan wannan taro dangane da halin da ake ciki a zirin Gaza.

Mark Regev Spoksman for israeli Prime Minister
Hoto: DW/Samar Karam

Gwamnatin Izraelan dai na la'akari da yiwuwar afkawa Gazan ta kasa, bayan lugudan boma bomai ta jiragen sama na tsawon mako guda a zirin na gaza. Harin da ya kasahe larabawan Palatinu akalla 430,bayan sama da dubu 2 da yanzu ke jinya.

'Yan ƙasashen ketare dake zaune a Gazan dai sun fara ficewa bisa ga korafin gwammantocinsu.Mark Regev shine kakakin gwamnatin Izraela.

Palästinenster in Gaza City Frau mit Gasflasche
Hoto: AP

"Mun saurari yadda gwamnatocin ketare ke kokawa danganbe da mutanensu da wannan rikici ya ritsa dasu a Gaza.Saboda bukatar hakane mukayi kokarin tattabatar da nasarar tsallakar dasu . Sai dai gwamnatin Izraela na iyakar kokarin na ganin cigaban kwararan kayayyacin agaji zuwa ga al'ummar Palastiwana"