1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine Wirtschaft

Usman ShehuMarch 4, 2014

Tattalin arzikin Yukren da kuma kasuwannin hada-hadar hannayen jari na cikin hain kila wa kala sakamakon rikicin da ake fama da shi bayan kutsen sojojin Rasha a Krimeya.

https://p.dw.com/p/1BJdk
Ukraine Soldaten Belbek Flughafen 04.03.2014
Hoto: Reuters

Rikicin siyasa da ke faruwa yanzu haka a Yukren bai yi illa ga kasuwannin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, kamar yadda tunda fari aka ji tsoron aukuwarsa. Bayan gigicewar da kasuwannin suka yi a Litinin da ta agabata, amma a wannan Talata al'amura sun sake dai-daituwa. To amma ga ƙasar Yukren kanta, ta na cikin wani mayuwacin hali na rashin kuɗi, muddi ba ta samu ɗauki daga ƙasashen waje ba.

A daidai lokacin da ƙasar Rasha ta tura dakaru izuwa ƙasar Yukren, su kuwa ƙasashen Turai nan take suka fara jin tsoro bisa samu iskar gas. Wanda dama aksari da ƙasar Rasha suka dogara.

Su ma dai kasuwannin shunku na lura da al'amuran da ke wakkana a ƙasar ta Yukren. Jörg Krämer shi ne jami'i mai kula da tattalin arziki a bankin Commerzbank da ke ƙasar Jamus.

Ukraine USA Außenminister John Kerry in Kiew Arseni Jazenjuk und Turchinov
Hoto: Reuters

"Tattalin arziki a zahiri na cikin barazana. Ina tunani musamman kan iskar gas. Domin ƙasashen Turai na samu ɗa bisa biyar na gas da suke amfani da shi daga ƙasar Rasha ne. Kuma ganin cikin ƙasar Yukren bututun ke rastawa, hakan na nufin bai fi rabin adadinda ake buƙata kawai za iya turawa ba, ta sauran bututun na daban. Kuma wannan sanin kowa ne, babban hatsari ne ga Tarayyar Turai"

Kasuwanni shunku dai a cikin sauri suka nuna jin jiki bisa rikicin na Yukren, inda kasuwar shunkun ƙasar Rasha ta faɗi da kashi 12 cikin ɗari a jiya Litinin, wanda shi ne faɗuwa mafi girma cikin shekaru shida. Haka zalika suma kasuwannin hada-hadar kuɗin Amirka da na Asiya dama na Turai, duk a Litinin da ta gabata sun samu faduwa. Bisa abinda Krämer yace kowa sun ɗimauta ne.

Ukraine Soldaten Perewalnoje 04.03.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/RIA Novosti

"Abinda ya kawo hakan shi ne rashin sanin tabbas. Domin akwai rashin sanin tabbas ga kasuwannin zuba jari da a yanzu ke tasowa. Domin tuni Amirkawa suka fara shiryawa irin siyasar da ta shafi kuɗaden duniya. Don haka tuni rikicin na ƙasar Yukren ya sa tsoro a jikin waɗannan masu zuba jari da a yanzu ke tashe. To amma idan aka yi magana kan kasuwannin duniya, zan iya cewa ɗimaucewar da aka yi ba mai yawa bace"

A yau Talata dai kasuwannin sun sake farfaɗowa, kama daga ƙasashen Turai, harma cikin ƙasar ta Rasha kanta, inda kudin ƙasar ya tsaya inda yake, musamman bayan babban bankin ƙasar ya ce ya daga kuɗin ruwa daga kashi biyar izuwa kashi bakwai cikin ɗari. A can ma ƙasar ta Yukren lamarin kasuwa ba yabo ba fallasa.

Ukraine Steinmeier in Berlin nach Gespräch mit Lawrow 04.03.2014
Hoto: John Macdougall/AFP/Getty Images

Rushewar tattalin arzikin Yukren tabbas zai shafi ƙasashe kamar su Jamus, wanda ta fi ƙarfin tattalin arziki a Turai. Domin kuwa kamfanonin Jamus na da jari a Yukren. Rainer Lindner shi ne jagoran wata cibiyar tattalin arziki a ƙasar Jamus da a sani da Ost-Auschuss.

"Hulɗar kasuwancin Jamus a Yukren ta kai kimanin Euro billiyan bakwai, wannan shekarunnan haka yake. Musamman a fannonin kamfanin ƙera motoci da na fasahar zamani, ƙasar Yukren na da mahimmanci a irin waɗannan ɓangarorin. A taƙaice dai muna da kamfanonin Jamus kimanin 500 dake aiki a Yukren, kuma dole su shiga tsoron abinda ke faruwa a ƙasar.

Ƙasar Jamus ita ce mafi gudanar da kasuwanci a Yukren bayan ƙasar Rasha. Don haka ne ake ganin rikicin ƙasar Yukren, zai yi babbar illa ga tattalin arzikin ƙasashen gabashin Turai.

Mawallafa: Johanna Schmeller/Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe