Rikicin Yuganda da Kwango | Siyasa | DW | 03.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Yuganda da Kwango

Jamus ta soke tallafin kuɗaɗe da ta ke bayar wa na kasafin kudi ga Yuganda saboda rahoton da MDD ta wallafa wanda ke zargi Yuganda da hannu a yaƙi Kwanko

Gwamnatin ta Yuganda ta ce ko kaɗan ba ta yarda da wannan zargi ba, wanda rahoton na kwamitin sulhu na MDD ya baiyana abin da ta ke kalon da cewar ƙarda kanzon kurege ne da kuma shafama ta kashin kaji. Ibrahim Abiriga na ɗaya daga cikin man'yan jami'an gwamnatin ya kuma yi tsokaci a kan rahoton da ya ce ba ya da tushe.Ya ce ''rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta fitar ba dai dai ba ne. Ba zamu mayar da martani a kan sa ba domin kuwa mun san cewar waɗannan ƙwararrun sun ƙirkiro labarun da ba za mu iya tabbatar da su ba ne.ya shugaban ƙasar mu dattijo ne a wannan yankin. Yana kuma ƙaumar zaman lafiya da ci gaba."

Shugaba Yoweri Museveni na da alaƙa da yan ƙabilar tutsit na ƙasashen Ruwanda da Kwango

President Yoweri Museveni of Uganda answers questions during a news conference following graduation ceremonies at Command and General Staff College in Fort Leavenworth, Kan., Friday, June 13, 2008. Museveni was at Fort Leavenworth to watch his son graduate. (AP Photo/Orlin Wagner)

Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda

An dai kwashe lokaci mai tsawo ana samun tashin hankali a yanki arewacin Kivu na Kwango inda yan tawayen ƙungiyar M23 suke tayar da bali saboda abin da suka kira rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2009.kuma shugaba Yoweri Museveni ya na da tarihin na daɗaɗiyar alaƙa da yan ƙabilar Tsusit na Ruwanda da Kwango waɗanda suka ficce daga ƙasaShen su zuwa Yugandar domin dafa sa ya kawar da mulkin Idi Amin Dada. Sannan kuma su ne waɗannan tsofin dakaru a wani lokaci suka shiga yaƙin basasar na Ruwanda domin kawo ƙarshen kisan kare dangin da ake yiwa yan ƙabilar Tutsi. A yau waɗannan tsofin bradan yan ƙabilar tutsit na Kwango da Ruwanda na riƙe da man'yan muƙamai na soji da yan' sanda a Yuganda.

Noah Achikule wani tsohon mayaƙi ne na Yuganda da ya yi aiki a acikin tsofuwar rundunar sojojin Yuganda tun lokaci Idi Amin Dada kafin ya koma cikin wata ƙungiyar yan tawaye a Kwango a yau jamii ne da ke saka ido akan harkokin zaɓe .Ya ce " Samar da gwamnati a ƙarkashin jagorancin ɗan ƙabilar Tutsi a Kongo, abin maraba ne ga Yuganda da kuma Ruwanda. kazalika, gwamnatin 'yan Tutsi a wannan ɓangare na jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo zai ba da damar cin gajiyar ɗimbin albarkatun ƙasar da ke wannan wurin. Za ta kuma kasance madogara - a duk lokacin da aka sami ruɗani ko dai a Yuganda ko kuma a Ruwanda."

Yuganda ta yi zaman sotar arzikin Kwango

Rwandan President Paul Kagame (L), his counterparts Yoweri Museveni (C) of Uganda and Joseph Kabila (R) of the Democratic Republic of Congo's (DRC) attend on November 21, 2012 a summit meeting at the Speke Resort in the Kampala suburb of Munyonyo. The leaders of the Democratic Republic of Congo, Rwanda and Uganda said on November 21 that the M23 rebels who have seized the eastern Congolese town of Goma must pull out immediately. The United Nations accuses Rwanda of backing M23 fighters who now control Goma, charges Kigali denies. Uganda has also dismissed charges it has aided the rebels. AFP PHOTO / PETER BUSOMOKE (Photo credit should read PETER BUSOMOKE/AFP/Getty Images)

Kagame da Museveni da Kabila a Goma

Ba shaka tun a ƙarshen shekara ta 1990 Yuganda ta riƙa satar albarkatun ma'adinai na Kwango abin da ya sa ma a shekara ta 2005 MDD ta ummarci Yuganda da ta biya diya ga irin ɓarna da ta yiwa Kwango, kuma katsa landon ɗin da shugaba Yoweri Museveni wanda ke da kusan shekaru 25 kan gadon muli ya ke yi akan harkokin mulki na ƙasar ta Kwango na neman cin gajiya kwai;Moses Odokonyero wani ɗan jarida ne a Yugandar.Ya ce " Shugaban Yuganda yana da muradu daban daban da ya ke son cimma. Ya na neman cimma biyan buƙatunsa a Somaliya, da Kongo kuma ya kasance wanda ke tsoma baki a cikin harkokin Ruwanda kamar yadda ya ke da hannu a harkokin Sudan Ta Kudu, kana yana da hannu dumu-dumu a jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Saboda haka - a zahiri, shi mutum ne wanda ke son fada .Dalilinsa na yin haka kuwa a fili ne, ya na son yin amfani da haka wajen cimma nasarar a lokacin daya ke shawarwari da ƙasashen yamma."

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Sauti da bidiyo akan labarin