Rikicin tawaye a kasar Myanmar | Labarai | DW | 20.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a kasar Myanmar

Sama da shekaru 20 kenan da kasar Bama ko kuma Myanmar ta tsunduma a cikin yakin basasa,wanda ya lakume dubban rayukan jama'an.

Rikicin tawayen da kasar Bama ko kuma miyammar ke fama da shi sama da shekaru 20,na dada kamari inda bangarorin gwamnati da na 'yan tawayen ke zargin juna da katse yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Disamban da ya shige. 'yan tawayen da keda manufar aware na yankin Kchin a kusa da iyaka da kasar China,na zargin hukumomin kasar ne da nuna musu wariya da kuma banbancin kabila. A ranar Juma'an da ta gabata ne,shugaban kasar ta bama Thein Sein ya kira bangarorin biyu da su dakatar da ba hamuta iska,to saidai kawo yanzu ana ci gaba da gobza kazamin fada a cewar James Lum Dau wani komandan rundunar tsaron kasar wanda ya zargi 'yan tawayen da yin fatali da kiran shugaban kasar na tsagaita wuta,yayinda 'yan tawayen suka ce sam ba za su lamunta da ajiye makaman ba matukar sojojin gwamnati na ci-gaba da kai musu hari. A nata bangare kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Watch ta bayana damuwarta inda ta zargi dakarun gwamnatin da kai hare hare akan yankunan masu gudun hijira. Sama da mutane dubu 120 ne suka kauracewa matsuguninsu a yankunan da ke ake fadan.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita: Usman Shehu Usman