1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin tawaye a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya

Abdoulaye Mamane Amadou
February 1, 2019

Bangarorin yan tawaye da gwamnatin Jamhuriyar tsakiyar Afirka, sun watse daga zaman tattaunawar ba tare da cimma wata maslaha ba

https://p.dw.com/p/3Cayl
Zentralafrikanische Republik UN Soldaten
Hoto: Reuters/B. Ratner

Masu aiko da rahotanni daga Sudan sun ce kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai da ke rike da kashi 80 cikin dari na kasar sun tashi baran-baran da gwamanatin ne bisa rashin cimma matsaya kan batun raba madafan iko, da batun yafe wa masu dauke da makamai a kasar. 

kawo yanzu kasar ta kulla yarjejeniyar sulhu akalla bakwai da 'yan tawaye daban-daban na kasar, tun lokacin da ta fantsama a cikin yakin basasa a shekarun 2012.