Rikicin tawaye a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya | Siyasa | DW | 27.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin tawaye a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya

Shugaba François Bozize ya nemi taimakon ƙasashen duniya domin yaƙar 'yan tawayen Seleka

Central African Republic President Francois Bozize arrives before the round table of the partners of the Central African Republic held in Brussels on June 17, 2011. AFP PHOTO JOHN THYS (Photo credit should read JOHN THYS/AFP/Getty Images)

François Bozize

Shugaban Jamhuriya Afrika ta Tsakiya François Bozize, ya yi kira ga ƙasashen Faransa da Amurika su taimaka masa, domin ya yaƙi 'yan tawaye wanda a halin yanzu ke gaf ga ƙwace Bangi babban birnin ƙasar.

Kimanin sati biyu kenan da saban rikicin tawaye ya ɓarke a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.Haɗin gwiwar 'yan tawayen Seleka sun tada bore sakamakon zargin da suke wa shugaba François Bozize da rashin cika alƙawuran da ya ɗauka a yarjejeniyar zaman lafiyar da suka rattaba wa hannu a shekara 2007 a birnin Libreville na ƙasar Gabon.

A tsukin sati biyu 'yan tawayen sun ƙwace birane da dama, kuma a yanzu sun doshi Bangi babban birnin Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Gondao Gilbert malami ne a jami'ar Bangi ya baiyana halin da mazauna birnin suka shiga a yanzu:A yanka hukumomin Bangi ba su rike da mulkin sauran sassan ƙasar. babu shigi da fici tsakanin sauran yankunan na kasa na babban birni, kuma duk mafin yawan kayan masarufi na shigowa daga cikin ƙasa.Idan wannan yanayi ya jima ,za mu shiga cikin matsanancin hali.

A jiya duban mutane sun shirya zanga-zanga a birnin Bangi, inda suka kai hari ga ofishin jikadancin Faransa, wanda su ke zargi da tallafawa 'yan tawayen Seleka.Yanzu haka hukumomin Paris sun jibge sojojin Faransa 250 a harabar ofishin jikadancin.

Itama ƙasar Amurika ta gargaɗi amurikawa da ke zaune a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya da su fice daga ƙasar,sannan Majalisar Dinkin Duniya ta dauke jam'ian wanda ba na cilas ba a wani mataki na kula da kaya ya fi ban cigiya.

A wata hira da yayi da DW Thierry Vircoulon na cibiyar ƙasa da ƙasa da sa ido akan rigingimu ya baiyana buƙatar 'yan tawayen Seleka:Mahimmin daga cikin buƙatocinsu shine aiwatar da yarjejeniyar da suka rattaba wa hannu tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2011.Wannan yarjejeniyar ta tanadi kwance ɗamara da kuma ɗaukar 'yan tawaye a cikin rundunonin soja na ƙasar.Ga alamu daga cimma wannan yarjejeniya zuwa yanzu, gwamnati ta yi burus da wannan alƙawura.

Baicin batun rashin cika alƙawuran da aka ɗauka Thierry Vircoulon ya bayana halin da jamhuriya Afrika ta Tsakiya ta shiga da rashin tsaro a sassa da dama na ƙasar da kuma zaman kashe wando ya samu gidin zama tsakanin matasa saban jini:

Wannan saban tawaye ya samo asuli daga tsafin 'yan tawaye a yankin arewacin ƙasar wanda suka mallaki makamai kuma su ke ɗaukar matasa cikin rundunoninsu.Sannan dakarun gwamnatin ƙasar Chadi da su ke taimakawa ta fannin tsaro a ƙasar, sun janye.Bugu da ƙari shekara mai kamawa ne rundunar ƙasashen yankin tsakiyar Afirka ta ke cika wa'adinta a jamhuriya Afrika ta Tsakiya.Wannan matsaloli sune su ka tattaru suka haddasa wutar da ke ci yanzu.

A wani jawabi da ya gabatar da safiyar yau, shugaba Franßois Bozize ya kira ga ƙasashen Amirka da Faransa su taimaka, saida a martanin da ya maida shugaban ƙasar Faransa François Holland, ya ce ƙasarsa ta daina shiga sharo ba shanu a rigingimun cikin gida na ƙasashen Afirka, to amma ya yi kira ga ɓangarorin biyu su tsagaita wuta,su kuma hau tebrin shawara.Bisa gayyatar ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin Afrika ta Tsakiya, nan bada jimawa ba, gwamnatin Bangi da 'yan tawayen Seleka za su komawa ƙasar Gabon domin tattanawa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas

Sauti da bidiyo akan labarin